Ba lalle baneba aga wata ranar talata mai zuwa ba, duba dalili>>>
Kwamitin duban wata na majalisar koli ta shari'ar Musulunci a Najeriya ta sanar da cewa ganin jinjirin watan Shawwal ranar Talata, 29 ga watan Ramadana da kamar wuya.
A bayanin da kwamitin tayi ranar Asabar a shafinta na Facebook, ta bayyana cewa an yi hasashen ko wata ya bayyana zai fito ne gabanin faduwar rana, saboda haka ba zai yiwu a ga jinjirin wata ranar Talata a Najeriya ba.
Amma duk da haka jama'ar Musulmi a fadin Najeriya su fita neman jinjirin wata saboda yin hakan ibada ne.
Ranar Talata, 11 ga Mayu ya yi daidai da 29 ga watan Ramadana da ake fara neman jinjirin watan Shawwal na shekarar 1442AH.
Wani sashen jawabin yace: "A ranar Talata, 29 ga Ramadana 1442AH (11 ga Mayu, 2021).. Tun da haihuwar jinjirin ba zai faru faru ba kuma wata zai fadi gabanin rana, hakan na nuna cewa ba zai yiwu a ga wata a Najeriya ranar Talata 11 ga Mayu, 2021 ba.
"Amma dai a sani cewa neman wata kowace ranar 29 ga wata ibada ne."
"Saboda haka a nemi wata ranar Talata."
Kwamitin ta kara da cewa duk wanda yayi ikirarin ganin wata, wajibi ne ya bada gamsasshen bayanin yadda ya gani.
Source: Legit
A ringa tabbatar da sahihancin magana dai kamin a yada ta ga al'umma
ReplyDeleteA ringa tabbatar da sahihancin magana dai kamin a yada ta ga al'umma
ReplyDelete