--
An haramta wa ƴan Indiya da Brazil da Turkiya shiga Najeriya Duba dalili

An haramta wa ƴan Indiya da Brazil da Turkiya shiga Najeriya Duba dalili


Gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin haramta wa matafiya da suka fito daga ƙasashen Brazil da Indiya da Turkiya shiga ƙasar saboda annobar korona.





Matakin wanda zai fara aiki ranar Litinin ya shafi duk wani jirgi da ya fito daga ƙasashen.





Sakataren gwamnati kuma shugaban kwamitin yaƙi da annobar korona Boss Mustapha ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa.





Matakin ya shafi biyan tarar dala 3,500 ga jirage da kuma fasinjan da suka saɓa dokar, kuma duk jirgin da ya ɗauko fasinjojin da ba ƴan Najeriya ba dole ya mayarsu.





Za a yi gwaji ga duk wanda ya fito daga ƙasashen tare killace waɗanda ke da shaidar zama Najeriya na tsawon mako ɗaya.





Source: Bbc Hausa




0 Response to "An haramta wa ƴan Indiya da Brazil da Turkiya shiga Najeriya Duba dalili"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?