
Zargin Ta'addanci: Dr. Pantami Zai maka Wasu gidajen Jaridu a Kotu,
Ministan sadarwa a Najeriya Sheikh Isa Ali Pantami ya ce zai maka jaridun da suka wallafa rahotan da ke alakanta shi da ta'ddanci a Kotu.
Sashen Bbc Hausa ya wallafa Cewa Sheikh Pantami ya mayar da martani ne bayan ɗaya daga cikin jaridun wato NewsWireNGR ta fitar da wasiƙar neman afuwan kan labarin da ta fitar da ke cewa Amurka ta sanya sunan ministan a jeren ƴan ta'adda.
1) @NewsWireNGR your RETRACTION through your independent investigation,has been noted. However, investigative journalism requires the investigation before publishing, not after.
— Isa Ali Pantami, PhD (@DrIsaPantami) April 12, 2021
Further, major publishers will meet my lawyers in the court on this defamation of character. https://t.co/08W3dP4tlf
Jaridar ta ce bayan ƙaddamar da bincike ta gano cewa labarin nata ba shi da tushe kuma bashi da alaƙa da Amurka don haka tana neman afuwan wanda ta ɓatawa suna da sauran masu karanta labaranta.
Jaridar ta bayyana cewa ta ɗauko labarin ne daga Daily Independent wadda ita ta soma wallafa wannan labarin.
Labarin na ikirarin cewa "Minista Pantami a baya yana yaba wa Abu Musab Al-Zarqawi a matsayin babban shugaba, wanda ya shiga ƙungiyar Al-Qaeda bayan ya yi hijira zuwa Afghanistan bayan harin da aka kai a Amurka na ranar 11 ga watan Satumbar 2001".
Batun dai ya ja hankali sosai tsakanin ƴan ƙasar musamman a shafukan sada zumunta.
Ministan dai ya ce za a haɗu a kotu domin sanin muhimmanci bincike a aikin jarida kafin wallafa kowanne irin labari.
0 Response to "Zargin Ta'addanci: Dr. Pantami Zai maka Wasu gidajen Jaridu a Kotu,"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?