
Yanzu yanzu: Shugaba Buhari ya nada sabon shugaban 'yan sandan Najeriya, duba sunansa da karin bayani gameda dashi anan>>
Tuesday, 6 April 2021
Comment
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin mataimakin sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, a matsayin sabon sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya. Ya maye gurbin Mohammed Abubakar Adamu, wanda wa’adin mulkinsa ya kare.
Ministan harkokin ‘yan sandan Najeriya, maigari Dingyadi ne ya sanar da hakan ga manema labaran gidan gwamnati.
A ranar 4 ga watan Fabrairun shekarar nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara wa’adin mulkin shugaban ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu. Alkali zai karba ragamar mulkin ‘yan sandan Najeriya ne a take.
Karin bayani na nan tafe…
Source: Legit
0 Response to "Yanzu yanzu: Shugaba Buhari ya nada sabon shugaban 'yan sandan Najeriya, duba sunansa da karin bayani gameda dashi anan>>"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?