--
Yanzu yanzu: Jiragen Yaƙin NAF Sun Jefa Wa Motar Sojojin Ƙasa Bam Bisa
Kuskure

Yanzu yanzu: Jiragen Yaƙin NAF Sun Jefa Wa Motar Sojojin Ƙasa Bam Bisa Kuskure


Jiragen yakin sojojin saman Nigeria, NAF, ya sakewa sojojin kasan Nigeria bam bisa kuskure a Mainok





Bam din da jirgin yakin ya saki ya yi sanadin rasuwar sojoji da dama tare da jikkata wasu - Wani babban soja ya ce an turo motar da aka sake wa bam din ne domin ta kawo wa sojoji ,





kafin aka sake mata bam bisa kuskure Sojoji da dama sun mutu bayan wani jirgin yaki na rundunar sojojin saman Nigeria ya saki bam kan dakarun sojojin kasa na Nigeria da ke Mainok a jihar Borno, Daily Trust ta ruwaito.





Majiyoyi daban-daban sun bayyana cewa sojoji 30 ne suka riga mu gidan gaskiya a Mainok. Wasu sojojin sun rasu ne sakamakon bam din da sojojin saman suka saki bisa kuskure yayin da wasu kuma yan ta'adda ne suka halaka su.





Majiya daga rundunar sojoji sun shaidawa majiyar Legit.ng cikin sirri cewa wasu kayayyakin sojoji sun bace ciki har da mota mai bindiga sakamakon artabun.





Tuni dai bidiyon harin ya bazu a shafukan intanet. Da aka tuntube shi a ranar Litinin, Kakakin rundunar sojojin sama, Edward Gabkwet ya ce shima ya ga bidiyon amma ba zai iya tabbatar da ingancinsa ba, yana mai cewa akwai bukatar yin bincike kwakwara.





"Da farko, sun mun tabbatar da ingancin bidiyon. "Ba zamu rikice ba kawai domin mun ga wani bidiyo a dandalin sada zumunta yana yawo. Sai mun tabbatar da ingancinsa.





"Idan sahihi ne, zai mu yi bincike kan me yasa ya faru da yadda ya faru. "Haka ake aikin. Ba zai yi wu ba kawai bayan na saurara in iye cewa sahihi ne ko akasin haka ba tare da an bi ka'idojin bincike ba,"





in ji Gabkwet. Wani babban soja da baya son a fadi sunansa ya ce motar da aka sakarwa bam din ta kawo sojoji ne domin taimakawa sojojin da ke artabu da yan ta'adda a Mainok.





Source: Legit


0 Response to "Yanzu yanzu: Jiragen Yaƙin NAF Sun Jefa Wa Motar Sojojin Ƙasa Bam Bisa Kuskure"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?