--
Yanzu-Yanzu: Hukumar INEC Ta Sanar Da Ranar Zaɓen Shekarar 2023

Yanzu-Yanzu: Hukumar INEC Ta Sanar Da Ranar Zaɓen Shekarar 2023


Hukumar zabe mai zaman kanta a Nigeria, INEC, ta sanar da cewa a ranar Asabar 18 ga watan Fabrairun ne za a yi zaben shekarar 2023 a kasar.





Shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin taron yini guda da aka gudanar don sauraron laifukan zabe na 2021 da kwamitin Majalisar Dattawa kan INEC ya shirya.





A cewar shugaban na INEC, saura shekara daya da watanni tara da makonnin biyu da kwana shida ko kuma kwanaki 660 a yi zaben daga yau.





"Kamar yadda dokar da ta kafa hukumar ta tanada, zaben zai kasance a ranar Asabar 18 ga watan Fabrairun 2023, ya rage saura shekara guda da watanni tara da sati biyu da kwanaki shida ko kwanaki 660 daga yau."









"Muna fatan za mu fitar da jadawalin zaben da zarar an kammala zaben gwamna na jihar Anambra wanda za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamban shekarar 2021.





"Don yin hakan, ya dace a samu tabbaci kan tsarin dokokin zabe don gudanar da zaben. Muna fatan Majalisar Tarayya za ta yi abin da ya dace a cikin lokaci," in ji Farfesa Yakubu.





Yakubu ya ce daya daga cikin ayyukan da hukumar ke yi shine gurfanar da wadanda suka saba dokokin zabe, wanda ya ce shine mafi wahala a cikin ayyukan INEC.





Ya koka da cewa rashin gurfanar da wadanda suka saba dokokin zabe cikin lokaci shine babban kallubalen da hukumar ke fama da shi tun kafuwarta.





Source: Legit




0 Response to "Yanzu-Yanzu: Hukumar INEC Ta Sanar Da Ranar Zaɓen Shekarar 2023"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?