--
Yanzu Yanzu: FG ta bada muhimmiyar sanarwa game da rijistar NIN, Duba
Abinda ta fada Anan>>>

Yanzu Yanzu: FG ta bada muhimmiyar sanarwa game da rijistar NIN, Duba Abinda ta fada Anan>>>


Gwamnatin tarayya ta samu ci gaba abin yabawa a kokarinta na samar da rumbun adana bayanai ga Najeriya Wannan ya kasance ne yayinda aka yi wa ‘yan kasa miliyan 51 rajistar NIN tun daga lokacin da aka fara ta a shekarar 2020





Gwamnati ta bayyana cewa an yi wa katin SIM miliyan 189 rijista zuwa yanzu Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis, 1 ga watan Afrilu, ta bayyana adadin ‘yan Najeriya da suka yi rajistan lambar shaidar zama dan kasa (NIN).





A cewar Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Ali Isa Pantami, akalla ‘yan kasa miliyan 51 ne ke da lambar NIN din su a yanzu, inji rahoton The Cable.









Pantami ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai na fadar gwamnati a Abuja a ranar Alhamis. Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Pantami ya kuma bayyana karara cewa doka ta tilastawa kowa shiga cikin shirin rajistar,





kuma rashin bin wannan umarnin na iya jawowa wasu rasa 'yancin asusun bankinsu da kuma ayyukan sadarwa. Har ila yau hakan na iya jawo yiwuwar zaman gidan yari na kimanin shekaru 14. Pantami ya ci gaba da bayyana cewa rajistar ta NIN ita ce hanya mafi kyau ta isa ga yawan mutanen kasar.





Har ila yau, Ministan ya bayyana cewa an yi rijistar SIM miliyan 189 ta hanyar shirin.





SOURCE: LEGIT.NG





 DAGA BZ NEWS 24/7





Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:





https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7





Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 





Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 





Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice





Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 





bzglobalservicelabari@gmail.com


0 Response to "Yanzu Yanzu: FG ta bada muhimmiyar sanarwa game da rijistar NIN, Duba Abinda ta fada Anan>>>"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?