--
Yanzu yanzu: Boko Haram Sun katse Network na MTN Da AIRTEL A Geidam

Yanzu yanzu: Boko Haram Sun katse Network na MTN Da AIRTEL A Geidam


Mazaunan garin Geidam a jihar Yobe sun waye gari babu daman kira mutane da wayoyinsu sakamakon katse wayoyin kamfanonin sadarwan MTN da Airtel da yan ta'addan suka yi Garin Geidam ne mahaifar mukaddashin Sifeto Janar na yan sanda, Usman Alkali, da kuma tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Geidam.





Da farko yan ta'addan sun kai hari garin da yammacin Juma'a, amma suka arce sakamakon ruwan wutan da Sojojin sukayi musu. Ali Maina, daya daga cikin mazaunan garin ya ce bayan da Sojojin suka wuce, yan ta'addan suka dawo, Daily Trust ta ruwaito.





Ya ce: "Sun aikata ta'asa a garin da safen nan. Muna ganin gidan na konewa kuma sun fasa shaguna suna kwashe kayen abinci."





"Abin ya fi bamu tsoro yanzu, saboda bamu san manufarsu ba. An yankemu daga layukan MTN da Airtel saboda sun yanke abin."





"Yanzu muna neman kariyan Allah ne, suna da motocin Hilux sama da 15." Bayan haka, kakakin hukumar yan sandan jihar Yone, Dungus AnduAbdulKarim ya tabbatar da sabon harin.





Source: Legit


0 Response to "Yanzu yanzu: Boko Haram Sun katse Network na MTN Da AIRTEL A Geidam"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?