
Yanzu Yanzu: Ana musayar wuta tsakanin Boko Haram da sojoji a Borno,
Ana musayar wuta tsakanin mayaƙan da ake zargi Boko Haram da sojoji a garin Damasak na jihar Borno.
A cewar wata majiyar sojoji, maharan na matukar neman karbe ikon garin, jaridar Daily Trust ta ruwaito. “Zan iya tabbatar da cewa sojoji ke da iko da garin Damasak amma ana ci gaba da fafatawa. Kun san tsawon wani lokaci yanzu, yan ta’addan sun addabi garin Damasak amma ba za su iya yin nasara ba saboda sojojin mu na nan a kasa,” in ji majiyar.
Haka kuma wata majiya ta JTF ta tabbatar da cewa an kwashe kusan awanni uku garin na karkashin hari. "Akwai bukatar dukanmu mu yi addu'a domin sojojinmu su yi nasara a kan wadannan mugayen mutane, Boko Haram sun koma Damasak bayan harin Asabar, kawai mu yi wa sojojin addu'a," in ji shi.
Wasu yan ta’adda sun kai hari a Damasak a karshen makon da ya gabata kuma akalla mutane shida aka kashe yayin da aka kona wasu gine-ginen jama'a.
Source: Legit
0 Response to "Yanzu Yanzu: Ana musayar wuta tsakanin Boko Haram da sojoji a Borno,"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?