--
Wata Sabuwa: Shahrarren Dan bindigan da ya tuba, Auwalu Daudawa, ya
koma gidan jiya

Wata Sabuwa: Shahrarren Dan bindigan da ya tuba, Auwalu Daudawa, ya koma gidan jiya


Shahrarren dan bindigan da ya jagoranci satan daliban Kankara 300, Auwalu Daudawa, ya koma daji bayan kimanin watanni uku da alanta tubarsa daga barandancin da satar mutane.





A cewar Daily Trust, wata majiyar jami'an tsaro da wasu majiyoyi na kusa da dan bindigan sun tabbatar da cewa Auwalu Daudawa ya koma dajin dake da iyaka da jihar Katsina.





Auwalu Daudawa ne ya jagoranci satan daliban makarantar GSS Kankara ranar 12 ga Disamba, 2020. Bayan watanni biyu da hakan , gwamnan jihar Zamfara ya sanar da cewa Daudawa ya tuba daga garkuwa da mutane kuma ya ajiye makamansa.





Daudawa da yaransa biyar sun mika bindigogin AK47 guda 20, harsasai barkatai, da roka 1.





Majiyoyi sun bayyana cewa Daudawa ya kwashe yaransa sun koma dajin Jaja, dake karamar hukumar Zurmi ranar Litinin.





"Ya kira daya daga cikin mutanensa a Gusau domin sanar da shi cewa ya isa dajin kuma ya yanke shawaran komawa harkar. Bai fadawa kowa kafin tafiyarsa ba,"





daya daga cikin majiyoyin ya fada. An ce Daudawa ya fusata ne saboda rashin cika alkawuran gwamnati bayan ajiye makamansa. Gwamnati ta baiwa Daudawa da yaransa wajen zama na tsawon makonni kafin aka saya masa gida a Damba, domin zamansa da iyalinsa.





"Gwamnati ke daukar nauyin ci da shansa. Ban san me yake bukata ba. Da yiwuwan ba'a cika mai alkawarin da akayi bane," daya daga majiyoyin jami'an tsaro ya bayyana.





Source: Legit




0 Response to "Wata Sabuwa: Shahrarren Dan bindigan da ya tuba, Auwalu Daudawa, ya koma gidan jiya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?