--
Wata Sabuwa: Naira Marley ya bada shawarar yadda mutum zai kammala
Alkur'ani a watan Ramadan,

Wata Sabuwa: Naira Marley ya bada shawarar yadda mutum zai kammala Alkur'ani a watan Ramadan,


Mawakin Nigerian nan Abdulaziz Fashola wanda aka fi sani da 'Naira Marley' ya bada wata kyakkyawar shawara ga musulmai a kafar sada zumuntarsa ta Twitter.





ya bada shawarar yadda musulmai zasu kammala Alkurani cikin kwaniki 30 na watan Ramadan mai alfarma.





Yace wadanda suke so su kammala karatun Alkuranin zasu rika karanta shafi 20 ne a kullum. Ya kara da cewa zasu rinka karanta shafi hudu-hudu a bayan kowacce sallar farilla.





Dandanan musulmai suka garzaya bangaren sharhi domin bayyana ra'ayinsu: @yinka cewa yayi: "kayi hakuri amma dole zan fadi wannan, kar kayi wasan zama mutumin kirki, matasa da yawa sun riga sun lalace da wakokinka." @raihaan yace:





"Lallai kam, sharhi akan abin musulunci yafi wanda bana musulunci yawa ba. Kar ka chanza saboda Ramadan, ya kamata kayi amfani da watan azumi ka chanza har abada.





@Inshiirah yace: "Ka samu Alqurani mai fassara ka karanta shi a yaran turanci aya bayan aya bayan kowacce ayar larabci…Zaka karu sosai.


Related Posts

0 Response to "Wata Sabuwa: Naira Marley ya bada shawarar yadda mutum zai kammala Alkur'ani a watan Ramadan,"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?