
Wata sabuwa: Amurka na zargin Najeriya da yin rufa-rufa kan kisan almajiran Sheikh Zakzaky
Wani rahoton Amurka kan batun kare hakkin dan adam a Najeriya na shekarar 2020 ya ce har yanzu babu wani karin bayani kan binciken gwamnatin tarayya ko kama wasu da ke da hannu a kashe-kashen da sojojin kasar suka yi wa mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky.
Amurka ta ce ya kamata zuwa yanzu Najeriya ta yi wani karin bayani ga duniya a kan zargin da ake yi wa dakarun sojin Najeriya na kisan almajiran Zakzaky kimanin 347, da kuma binne su a manyan kaburbura domin boye abin da aka aikata, BBC ta rahoto.
A shekarun baya ne rikici ya barke tsakanin sojojin Najeriya da almajiran Sheikh Zakzaky, lamarin da ya jawo mutuwar da dama daga cikin almajiran.
Ana zargin sojojin Najeriyan da kisan da dama daga cikin almajiran. Hakazalika aka tsare jarogaran Shi'a na Harkar Musulunci a Najeriya, Sheikh Zakzaky na tsawon shekaru a gidan yari.
Barka Da Zuwa Bz News 24/7:
Shin Kana Buqatar Musanar Dakai Zafafan Labaran Abinda Ke Faruwa A Najeriya Dama Duniya Baki Daya Akoda Yaushe?
Idan Kana Buqata Kasance Damu a Group Dinmu Na WhatsApp Ta Hanyar Shiga Yanzu👇
https://chat.whatsapp.com/Cl3ssMEUvovLoTJ3ReHz5D
Kasance Cikin Jerin Masu Tayamu Yada Wannan Shafin ga Sauran Al-ummah Kayi Copy Na Adreshin mu Ka yada ga Sauran Al-ummah ga Adreshin 👇
https://www.bzglobalservice.com.ng
0 Response to "Wata sabuwa: Amurka na zargin Najeriya da yin rufa-rufa kan kisan almajiran Sheikh Zakzaky"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?