--
Wata Kungiya daga kudu ta aikewa Kasar Amurka sakon a binciki Sheikh
Pantami

Wata Kungiya daga kudu ta aikewa Kasar Amurka sakon a binciki Sheikh Pantami


Wata Kungiya daga kudancin Najeriya ta aikewa kasar Amurka da neman a binciki sheikh Pantami kan zargin alakantashi da aka yi da Ta’addanci.





Kungiyar me zama kanta me sunan Concerned Nigerians wadda Deji Adeyanju ke jagoranta ta nemi kasar ta Amurka ta binciki Ministan Sadarwa da tattaTat Arzikin Zamani Sheikh Isa Ali Pantami kan zarge-zargen da ake masa.





Ta nemi cewa idan dai wadannan zarge-zarge sun zama Gaskiya to tana neman a sakashi cikin wanda za’a sakawa Ido na dindindin, kamar yanda Punchng ta ruwaito.





Sheikh Pantami dai na fuskantar kalubale sosai inda wasu ke alakanta hakan da tsare-tsaren gyara da ya dauko kan harkar sadarwa, wadda wasu ke ganin za’a takura musu.






0 Response to "Wata Kungiya daga kudu ta aikewa Kasar Amurka sakon a binciki Sheikh Pantami"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?