--
Tirkashi: Mahaifiyar amarya ta tsere da sadakin diyarta, ta bar madaura
aure da Lahaula

Tirkashi: Mahaifiyar amarya ta tsere da sadakin diyarta, ta bar madaura aure da Lahaula


Mahaifiyar amaryar ta gudu da kudin sadakin diyarta a ranar daurin aure bayan komai ya kankama





Anne Maweni, ta zargi dangin mahaifin diyarta da kokarin danne kudin sadakin har Sh170,000 don haka ta gudu





An nemeta an rasa amma daga bisani tayi sakon kar ta kwana ta wayar 'yar uwarta cewa a cigaba da biki kawai An yi wata karamar hatsaniya wurin biyan sadaki bayan an gano cewa mahaifiyar amarya tayi sama da fadi da kudin sadakin da sirikanta suka kai.





Mahaifiyar amaryar mai suna Anne Maweni, an gano cewa ta yi tsammanin iyayen amaryan zasu yi mata mugunta, lamarin da yasa ta tsere da sadakin da ya kai Sh170,000.





An fara shirin auren a Garsen, yankin Tana River dake Kenya yayin da 'yan uwa suka cewa, Maweni, mahaifiyar amaryar bata nan, The Nation ta ruwaito.





"Da aka fara bikin, ita ta baiwa baki da dattawa abinci amma sai bata zauna tare da su ba. babu wanda ya san lokacin da ta gudu," Veronica Meily, 'yar uwar Maweni ta sanar.





Duk kokarin samunta da aka yi a waya ya gagara saboda wayarta a kashe take. Daga bisani Maweni ta tura sakon kar ta kwana ga kanwarta ta wata lamba inda tace ta jagoranci daurin auren da bikin.





Daga nan ne dattawa da sirikan dake zaune suka gane cewa akwai wata matsala. Daga bisani Maweni ta sanar da cewa tayi hakan ne saboda sun bar ta da 'ya'yan bayan rasuwar mahaifinsu kuma babu mataimaki, amma aure ya tashi sun zo kwasar rabonsu.






Related Posts

0 Response to "Tirkashi: Mahaifiyar amarya ta tsere da sadakin diyarta, ta bar madaura aure da Lahaula"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?