
Sheikh Ahmad Gumi ya Bayyana Dalilin da ya sa na ya daina sulhu da yan bindiga,
Sheikh Ahmad Mahmoud Gumi ya kwana biyu bai shiga daji ganawa da yan bindiga ba Wannan ya biyo bayan caccakan da wasu mutane suke masa
Sheikh Gumi ya ce kawai ya daina ne saboda matsayar da gwamnatin jihar ta dauki Shahrarren Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa ya daina sulhu da yan bindiga ne saboda gwamnatin jihar ta nuna ba ta son haka.
Wannan ya biyo bayan harin da yan bindiga suka kai jami'ar Greenfield dake hanyar Abuja-Kaduna inda sukayi awon gaba da dalibai kuma suka kashe mutum daya.
Yan bindigan sun bukaci N800m a matsayin kudin fansa. Yayin magana da SaharaReporters ranar Alhamis, hadimin Gumi, Salisu Hassan, ya ce Malamin ya daina tafiya sulhu da yan bindigan ne don bin umurnin gwamnatin jihar.
"A'a, Sheikh ba wai yana da wasu ayyuka bane. Matsalar itace gwamnati ta ce bata son a yi sulhu da wadannan mutane," Hassan yace.
"Saboda haka Sheikh yana kokarin samar da wasu hanyoyin cimma manufarsa. Gwamnatin jihar ta ce ba ta son sulhu."
Za ku tuna cewa Gumi ya shiga dazuka daban-daban a Arewa maso yammacin Najeriya don yiwa yan bindiga wa'azin suun ajiye makamansu, su yi sulhu da gwamnati,
amma El-Rufa'i ya nuna baya son hakan. Gwamnan jihar ya ce zai hukunta duk wanda yayi sulhu da yan bindiga da sunan gwamnati.
0 Response to "Sheikh Ahmad Gumi ya Bayyana Dalilin da ya sa na ya daina sulhu da yan bindiga,"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?