
Saurayi ya kashe Kakarshi ya gundule kanta ya kai ofishin yansanda
Wednesday, 7 April 2021
Comment
Wani matashi ya kashe Kakarshi kuma ya gundule kanta ya saka a cikin laida ya kai ofishin yansanda na Kisumu a kasara Kenya ranar 5 ga watan Aprilu.
Wannan lamari ya haifar da mamaki tsakanin yansanda. Sai dai yansanda sun dauki saurayin a cikin motocinsu suka tafi rukunin gidajen Nyalenda inda saurayin ya kashe tsohuwar.

Yansanda sun dauki gawar tsohuwar suka kai dakin ajiye gawa a Asibiti domin gudanar da binciken Postmortem, yayin da suka damke saurayin kuma suka ci gaba da gudanar da bincike.
DAGA ISYAKU.COM
0 Response to "Saurayi ya kashe Kakarshi ya gundule kanta ya kai ofishin yansanda"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?