
Ramadan Kareem: Yana Gidan Kurkuku Ya rabawa Mabukata Tallafi- Sheikh Zakzaky
Duk da kasancewarsa a garkame, shugaban kungiyar Shi'a Zakzaky ya raba kayan abinci a Ramadana
Dansa ne ya jagoranci rabon kayayyakin abincin a wasu sassan kasar ciki har da mahaifarsa Zariya
Dan sa ya kuma bayyana cewa, wannan aiki ne da baban nasa ke yi na tsawon shekaru kuma ba zai daina ba Shugaban Mabiya Shi’a na Kungiyar Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (IMN),
Ibraheem Zakzaky ya raba kayan abinci na miliyoyin Nairori ga mabukata albarkacin watan Azumin Ramadan, Aminiya ta ruwaito
Dan sa Muhammad Ibraheem Zakzaky ne ya jagoranci shirin rabon kayan abincin da suka hada da buhunan Shinkafa da Sukari da Masara da Gero a madadin mahaifin nasa.
Awata takarda da ya sanya wa hannu, Muhammad Ibraheem Zakzaky ya ce mahaifin nasa ya bayar da umarnin rabon kayan Azumin ne ga mabukata.
Ya ce, “Mahaifina wanda yanzu haka yake tsare a gudan kurkuku, shine ya bayar da umarnin raba kayan abincin don a tallafawa mabukata a Najeriya a watan Azumin Ramadana mai Albarka.
“An kammala rabon kayan a Zariya dake jihar Kaduna da wasu Kananan Hukumomin dake fadin jihar kuma wannan wani aiki ne da mahaifin nawa ya kwashe kusan shekaru 20 yana yinsa.
“Zai ci gaba da yin haka ko da bayan gwamnatin Buhari ta shude wadda ta kashe dumbin mabiyansa da suka hada ’ya’yansa uku da aka kashe,” inji shi.
Muhammad ya kara da cewa, Malamin na taya daukacin al’ummar Musulmin duniya murnar zagayowar watan Ramadana tare da tabbatar musu da cewa suna cikin addu’o’insa a wannan wata na Azumi.
Bugu da kari, an rarraba kayan abincin a matsugunan ’yan gudun hijira dake jihohin Katsina da Zamfara. Sauran Jihohin da suka amfana da rabon sun hada da Sakkwato da Kebbi da Kano da Filato da Nasarawa da kuma jihar Bauchi.
0 Response to "Ramadan Kareem: Yana Gidan Kurkuku Ya rabawa Mabukata Tallafi- Sheikh Zakzaky"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?