
Mijina Ya sakeni Matar Aure ta koka ta nemi Taimako a Tiwita Duba Abinda tace Anan>>>
Wata mata yar Najeriya da ta zana hoton Ahmed Bola Tinubu a jikinta ta ce mijinta ya fitittiketa daga gida mlkk
Matar mai suna @AyokunmiBabato1 a Tuwita ta yi kira ga yan Najeriya su kawo mata dauki - A cewarta, ba tada wajen zuwa kuma dukkan yan'uwanta sun kaurace mata saboda abinda ta aikata Matar da ta zana hoton babban jigon jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Ahmed Tinubu a gadon bayanta ta kai kuka kafafen ra'ayi da sada zumunta bayan mijinta ya koreta daga gida.
Matar ta ce bayan da mijinta ya fitittiketa, yan'uwanta sun ce ba zasu yarda ta dawo gidansu ba. Saboda haka ta garzaya shafinta na Tuwita don kira ga mutane su taimaketa, ba tada wajen kwana. Matar mai suna @AyokunmiBabato1 a Tuwita tace: "Mijina ya fitittikeni daga gida saboda zanen da nayi kuma ba ni da wajen zuwa. Ku taimakeni."
My husband sent me out of the house because of the tattoo I draw and I don't even have anywhere to go. Please help me 😭 pic.twitter.com/BrubkVFB7X
— Tollyfaz (@AyokunmiBabato1) March 31, 2021
0 Response to "Mijina Ya sakeni Matar Aure ta koka ta nemi Taimako a Tiwita Duba Abinda tace Anan>>>"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?