
Mako biyu da yin aurenta amarya ta fara korafi, ta ce mijinta yana aikenta barkatai
Abena Moet wacce ta yi aure kasa da makonni uku ta ba mutane da yawa mamaki a shafukan sada zumunta da cewar da tayi babu wani abu na musamman game da aure
A wani bidiyo mai ban dariya, ta ambaci cewa a cikin aure, kawai miji na aiken matar ne yadda ransa yake so
An gano ta a cikin bidiyo tana kallon kafadunta don tabbatar da cewa mijinta baya sauraron abunda take fadi Shahararriyar matashiyar nan ta kasar Ghana,
Abena Moet, ta haddasa cece kuce game da ra’ayinta a kan aure bayan shafe kusan makonni uku a gidan miji.
A cikin bidiyon barkwancin da ke yawo a shafukan sada zumunta, Abena Moet ta nuna cewa daga abin da ta gani, da zaran kin yi aure a matsayinki na mace, toh kawai mijinki zai ta aikenki ne yadda ransa ke so.
An gano ta a bidiyon tana kallon kafaɗarta don tabbatar da cewa sabon mijin nata ba ya jin abunda take fadi a bidiyon nat Abena Moet ta yi aure a wani kasaitaccen biki da ya bazu a yanar gizo a ranar 27 ga waran Maris, 2021.
0 Response to "Mako biyu da yin aurenta amarya ta fara korafi, ta ce mijinta yana aikenta barkatai"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?