--
Karya akayi min, ban ce za'a kulle wanda yaki yin NIN shekaru 14 ba: Dr
Isa Pantami Yayi martani

Karya akayi min, ban ce za'a kulle wanda yaki yin NIN shekaru 14 ba: Dr Isa Pantami Yayi martani


Ministan Sadarwa, Dr Isa Ali Pantami, ya karyata rahoto dake yaduwa cewa yace duk wanda bai da lambar katin zama dan kasa NIN zai ci zaman gidan yari na tsawon shekaru 14.





Pantami ya bayyana cewa ko sau guda bai ambaci hukuncin daurin shekaru 14 ba. Kawai abinda ya fadi shine an kafa hukumar NIMC na tsawon shekaru 14 yanzu.





Hakazalika ya kalubalanci wata kafar jaridar da ta wallafa labarin cewa ta saki bidiyon inda ya fadi hakan.





Wadannan mumunan fassara ne. Pantami bai ambaci daurin shekaru 14 ba. Amma yace NIMC ta kwashe shekaru 14 da kafa ta, tun 2007.





Tun da yan jarida sun shaida jawabin, kamata yayi a saki bidiyon ga mutane su gani," ya bayyana a shafinsa na Tuwita.









A bangare guda, Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis, 1 ga watan Afrilu, ta bayyana adadin ‘yan Najeriya da suka yi rajistan lambar shaidar zama dan kasa (NIN).





A cewar Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Ali Isa Pantami, akalla ‘yan kasa miliyan 51 ne ke da lambar NIN din su a yanzu. Pantami ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai na fadar gwamnati a Abuja a ranar Alhamis.





Barka Da Zuwa Bz News 24/7:





Shin Kana Buqatar Musanar Dakai Zafafan Labaran Abinda Ke Faruwa A Najeriya Dama Duniya Baki Daya Akoda Yaushe?





Idan Kana Buqata Kasance Damu a Group Dinmu Na WhatsApp Ta Hanyar Shiga Yanzu👇
https://chat.whatsapp.com/Cl3ssMEUvovLoTJ3ReHz5D





Kasance Cikin Jerin Masu Tayamu Yada Wannan Shafin ga Sauran Al-ummah Kayi Copy Na Adreshin mu Ka yada ga Sauran Al-ummah ga Adreshin 👇
https://www.bzglobalservice.com.ng


0 Response to "Karya akayi min, ban ce za'a kulle wanda yaki yin NIN shekaru 14 ba: Dr Isa Pantami Yayi martani"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?