--
Kalli Hotuna: Mohammed Adamu ya sauka a hukumance, ya mika mulki ga
sabon IGP Usman Baba

Kalli Hotuna: Mohammed Adamu ya sauka a hukumance, ya mika mulki ga sabon IGP Usman Baba


Sufeto janar na 'yan sanda mai barin gado (IGP), Mohammed Adamu, ya mika shugabanci ga sabon IGP mai rikon kwarya, Usman Alkali Baba.
A cewar jaridar PM News, an gudanar da bikin mika shugabancin ne a hedikwatar rundunar da ke Abuja a ranar Laraba, 7 ga Afrilu.





Jaridar The Nation wacce ita ma ta ruwaito





rahoton ta bayyana cewa Adamu ya mika mulki bayan Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya yiwa Baba ado da sabon mukamin sa a Fadar Gwamnati, Abuja.
Da farko Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya yiwa sabon Sifeto Janar na yan sanda kwalliya da karin girma zuwa IGP.









Za ku tuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya amince da nadin Usman Alkali Baba a matsayin sabon shugaban yan sanda.





Wadanda ke hallare a bikin kwalliyar sun hada da IGP mai barin gado, Mohammed Adamu; Sakataren gwamnati, Boss Mustapha; da Ministan harkokin yan sanda, Maigari Dingyadi.









Sauran sune Malam Garba Shehu; Laolu Akande; Sakataren fadar shugaban kasa, Tijjani Umar da sakataren ma'aikatar yan sanda.


0 Response to "Kalli Hotuna: Mohammed Adamu ya sauka a hukumance, ya mika mulki ga sabon IGP Usman Baba"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?