--
Kalli Hotuna da bidiyon kasaitaccen bikin mutuwar aure da wata yar
Najeriya tayi,

Kalli Hotuna da bidiyon kasaitaccen bikin mutuwar aure da wata yar Najeriya tayi,


Wata yar Najeriya, Ikea Bello, ta yi fice a kafafen sada zumunta bayan ta yi wani abin da ba a saba gani ba, mai koyar da rayuwar ta yi bikin mutuwar aurenta cikin kasaita





Ta yi gagarumin liyafa yayin da take murnar samun yancinta tare da abokai da masu fatan alheri Mutane biyu kan kulla aure tare da fatan alkhairi,





amma rayuwa ta kan sauya abubuwa zuwa hanyar da ba a yi tsammani ba. Wannan shi ne lamarin wata likita yar Najeriya, Ikea Bello.





A kwanan nan ne Bello ta sanya ‘yan Najeriya a shafukan sada zumunta cikin al’ajabi bayan ta yi gagarumin biki don murnar rabuwa da mijinta.





A shafukan zumunta, ƙwararren mai horar da rayuwar ta wallafa hotuna da bidiyon kasaitaccen bikin.





Ya bayyana an zabi kalar suturar da za a sa ganin yadda kawayen matar suka sanya jajayen kaya.





Ikea Bello kuma ta saka wata kayatacciyar karammiski mai kalar shuni da ja kuma an ganta tana shakatawa tare da baƙinta.





A cewarta, mutuwar aurenta da bikin 'yancin ya kasance abin birgewa. A cikin kalmomin ta, abun ya kayatar. Bello ta yi shirya bikin kamar wani sabon bikin aure.





Ta canza kayanta har ma ta bayyana cewa zabin kayan da tayi na farko ya samu karbuwa ne daga yar wasan Nollywood, Tonto Dikeh.





Duk da rashin bayyana ainahin abin da ya haifar da mutuwar auren nata, ta bar wasu alamu a cikin maudu’inta inda ta bayyana cewa ta rabu da mai yada jita-jita kuma cewa ta tsira daga zamantakewar mai guba.





Kalli hotuna daga wallafarta a kasa:














0 Response to "Kalli Hotuna da bidiyon kasaitaccen bikin mutuwar aure da wata yar Najeriya tayi,"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?