--
Kalli Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura ya
gudana a kasar Masar

Kalli Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura ya gudana a kasar Masar


Ranar Asabar 3 ga watan Afrilu ne kasar Masar ta gudanar da wani gagarumin bikin sauyawa tsoffin Fir'aunonin kasar kaburbura zuwa wani katafaren gidan adana kayan tarihi.
An yi jerin gwanon Fir'aunonin cikin kasaita, yayin dubban dubatan mutanen kasar suka yi dafifi a yayin bikin.





An makudan miliyoyin daloli domin bikin na nuna girmamawa ga kaburburan masu dunbun tarihin da ya haura shekaru sama da 3,000, in ji Rahoton Aljazeera.





An sauyawa Fir'aunonin 22 wajen zama, wadanda suka kasance 18 daga cikinsu wasu shahararrun sarakunane da kuma sarauniyoyi hudu.





Hukumomin kasar ta Masar ta rufe manyan hanyoyin da suka dangana da kogin Nilu domin nuna girmamawa ga a Fir'aunonin.





A tarihance, kasar na matukar alfahari da ajiyar sauran gawarwakin Fir'aunonin na tsawon tarihi.













Ga wasu daga cikin hotunan yadda bikin ya gudana a jiya Asabar.





Kalli Bidiyon A Qasa:






0 Response to "Kalli Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura ya gudana a kasar Masar"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?