
Kalli Bidiyo Da Hotunan Wani Ɗan Chadi Da Aka Kama Yana Sayarwa Da 'yan Boko Haram Miyagun Ƙwayoyi

Jami'an hukumar NDLEA sun kama wani mutum ɗan ƙasar Chadi da ke sayarwa yan ta'addan kwayoyi - An kama Adama Uomar Issa ne a garin Taraba ɗauke da miyagun kwayoyi cikin jakuna da takalman Mata
Shugaban NDLEA, Mohammed Buba Marwa ya yabawa jami'an ta bukaci su cigaba da jajircewa Jami'an hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, NDLEA, ta kama wani mutum mai shekara 35 ɗan ƙasar Chadi da ke sayar wa ƴan ta'adda miyagun kwayoyi.

An kama wanda ake zargin, Adama Uomar Issa a jihar Taraba ɗauke da miyagun ƙwayoyi daban-daban, TVC ta ruwaito.
Sanarwar da kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya fitar ta ce an kama wanda ake zargin, Adama Uomar Issa, a ranar Laraba, 31 ga watan Maris a Jalingo, jihar Taraba tare da Tramadol mai 225mg da 250mg wanda nauyinsu ya kai 21.70kg.
An kuma kwato Exol. 5; 100,050 France CAF da N61,000. Babafemi ya ce kwamandan NDLEA a jihar Taraba, Suleiman Jadi, ya ce wanda ake zargin yana magana da harsunan Faransanci da Larabci ne kuma ya yi ikirarin cewa zai tafi da haramtattun kayan zuwa Chadi ne kafin aka kama shi a Jalingo.

Ya ce bincike ya nuna cewa shi babban dilalin miyagun kwayoyi ne na Boko Haram. Babafemi ya ce an ɓoye muggan ƙwayoyin da aka siyo daga Onitsha jihar Anambra a cikin sabbin jakunkunan mata da takalma.
Ga bidiyon a kasa:
#DrugWar One of the suspects, Adama Uomar Issa, was arrested on Wednesday, 31st March, 2021 in Jalingo, Taraba State with 21.70Kg of Tramadol 225mg and 250mg.
— TVC News (@tvcnewsng) April 1, 2021
Also seized from him were 15.7Kg of Exol.5; 100,050 France CAF and N61, 000.@ndlea_nigeria @PoliceNG https://t.co/vBDbYebbxY pic.twitter.com/HmaJbp7HFt
SOURCE: LEGIT.NG
DAGA BZ NEWS 24/7
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Kalli Bidiyo Da Hotunan Wani Ɗan Chadi Da Aka Kama Yana Sayarwa Da 'yan Boko Haram Miyagun Ƙwayoyi"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?