--
Kai Tsaye: duban jinjirin Watan Ramadan ya fara gudana Yau A kasar
Saudiyya,

Kai Tsaye: duban jinjirin Watan Ramadan ya fara gudana Yau A kasar Saudiyya,


Kotun kolin Saudiyya ta ba da umarnin a fara duban jaririn wata Ramadana daga ranar Lahadi 29 ga watan Sha'aban kamar yadda kalandar Umm Al Qura ta bayyana.





Idan ba a ga watan ba a ranar 29 to babu shakka ranar 30 ga watan Sha'aban za a bada umarnin a tashi da azumin watan Ramadana.





Kamar yadda yake cikin koyarwar addinin Islama idan ba a ga watan ba a ranar 29 to 30 ga wata za a dauki azumi domin kuwa watannin musulunci ba sa yin 31.





A ko wacce shekara Saudiyya na da hukumar duban wata da ke jan ragammar wannan aiki, ta hanyar amfani da na'urorin zamani.





Ka zalika dukkanin kasashen musulmai za su fara duban nasu watan daga ranar 29 ga watan Sha'aban domin fara Azumin watan Ramadana mai albarka.






0 Response to "Kai Tsaye: duban jinjirin Watan Ramadan ya fara gudana Yau A kasar Saudiyya,"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?