--
Fusataccen Magidanci ya kashe Liman bisa zargin kwanciya da amaryarsa

Fusataccen Magidanci ya kashe Liman bisa zargin kwanciya da amaryarsa


Rundunar yansandan jihar Niger ta kama wani magidanci mai suna Umar Jibril wanda aka fi sani da suna "ba dama" bisa zargin kashe babban Limami na Edati ta hanyar amfani da karfe sakamakon zargin da ya yi wa Liman da kwanciya da Amaryarsa. Kamar yadda isyaku.com ya ruwaito.
Yayin tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin yansandan jihar Niger Adamu Usman ya ce wanda ake zargi ya aikata laifin ne ranar Litinin 12 ga watan Aprilu.





Ya ce wanda ake zargin ya gaya wa yansanda lokacin bincike cewa Limamin yana zina da matarsa. Ya ce ranar da lamarin ya faru da yamma, yana hutawa a kofar gidansa, sai ya gan Liman ya wuce shi ya bi ta gidan makwabcinsa.





Ya ce a daidai wannan lokaci Amaryarsa mai suna Aishatu Umar ta fito ta ce za ta je ta yi bahaya a gefen gidansu. Amma bayan ya jira har tsawon wani lokaci bata dawo ba, sai ya zagaya nemanta. Daga bisani sai ya ji muryarta a gidan makwabcinsa.





"Na shiga daki na sami Liman tsirara kwance a kan gado tare da Amarya ta. Suna barci tare, ban yi komai ba sai na fita daga cikin dakin. Na tafi gidan dan uwa na sai na gaya masa abin da na gani". A cewar Umar.





Ya ce ya kasa rike fushi da bacin ransa ne bayan Liman ya kira shi domin su yi sulhu a kan matsalar.





"A lokacin da muke tattaunawa kan matsalar da Liman, lamarin ya yi zafi, mun yi zafafan muhawwara da juna, sakamakon haka na kwace wani karfen rodi daga hannun Alhaji Hassan sai na caka wa Liman a wuya" Inji Umar.





Shugaban yansandan jihar Niger ya ce za su gurfanar da Umar a gaban Kotu ba tare da bata lokaci ba.





DAGA ISYAKU.COM


Related Posts

0 Response to "Fusataccen Magidanci ya kashe Liman bisa zargin kwanciya da amaryarsa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?