--
EFCC ta kama tsohon gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari

EFCC ta kama tsohon gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari


Hukumar EFCC a yanzu haka tana yi wa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari tambayoyi kan wasu zarge-zargen cin hanci da rashawa





An tattaro cewa an rike tsohon gwamnan a ofishin hukumar na Sakkwato na tsawon awanni takwas har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton a ranar Talata, 20 ga watan Afrilu





Majiya ta ce an bayar da belin Yari amma bai iya cika sharuddan belin ba Jaridar Premium Times ta rahoto cewa yanzu haka tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, yana hannun hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC).





A cewar rahoton, jami'an EFCC na yi wa Yari wasu tambayoyi kan zarge-zargen cin hanci da rashawa.





An ce an tsare tsohon gwamnan a ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa na Sakkwato tsawon awanni takwas a daidai lokacin rubuta wannan rahoton.





majiya da aka nakalto a cikin rahoton ta ce: “Ya amsa gayyatar a ofishin Sakkwato da misalin karfe 11 na safiyar Talata. An basa beli, amma bai iya cika sharuddan belin ba.”


0 Response to "EFCC ta kama tsohon gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?