--
Duba Jerin Mutane 12 da Zasu Iya Shan Azumi a Ramadana

Duba Jerin Mutane 12 da Zasu Iya Shan Azumi a Ramadana


Watan Azumin Ramadana wata ne mai falala da ake azumtar kwanaki 30 a jere ba ci ba sha da rana Azumi na da hukunce-hukunce, ciki har da wadanda suke magana kan ajiye Azumin ko yinsa,





Malamin addinin Islama, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana wasu hukunce-hukuncen yin Azumin Azumin watan Ramadana na daga cikin ibadun da aka wajabta wa Musulmai, sai dai akwai wasu mutane 12 da aka ba su damar ajiye azumin, ko da yake hukunce-hukuncensu sun bambanta.





A wani bidiyo da BBC Hausa ta wallafa, daya daga cikin malaman addinin Musulunci a Najeriya Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana wasu mutune 12 da aka yi musu uzurin su ajiye azumi a watan Ramadana.





A cewar sa, wasu daga cikin mutanen za su rama Azumin, wasu kuwa ciyarwa za su yi, yayin da wasu ba za su ciyar ba kuma ba za su yi ramuwa ba.





Wadanda za su rama Azumi:





1. Mace mai jinin al'ada





2. Matar da ta sha Azumi saboda jinin biki





3. Matafiyi





4. Mara lafiya





Wadanda za su ciyar:





5. Mace mai ciki





6. Mace mai shayarwa





7. Mai ciwon kishirwa





8. Mai ciwon 'yunwa





Wadanda ba za su rama ba, kuma ba za su ciyar ba:





9. Yaro





10. Mahaukaci





11. Tsofaffi





12. Mai ciwon farfadiya





Source: Legit


0 Response to "Duba Jerin Mutane 12 da Zasu Iya Shan Azumi a Ramadana"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?