
Daga Neman gira anrasa Ido: Mutum bakwai 7 sun mutu Bayan anyi Musu Allurar rigafin korona
Jami'iyar kula da lafiya a Burtaniya a ranar Asabar ta ce mutane bakwai cikin 30 da suka yi fama da daskarewar jini bayan sun karbi allurar rigakafin Korona ta Oxford-AstraZeneca, sun mutu.
Amincewar da Burtaniya ta yi game da mutuwar ta zo ne yayin da kasashen Turai da yawa suka dakatar da amfani da allurar ta AstraZeneca kan hadarin daskarewar jini, Daily Trust ta ruwaito.
Rahoton da likitoci ko kuma jama'ar gari suka gabatar ta shafin yanar gizon gwamnati, ya zo ne bayan an yi allurai miliyan 18.1 na rigakafin a kasar.
Mafi yawan lokuta (22) sun kasance batu kan yanayin daskarewar jini wanda ake kira cerebral venous sinus thrombosis.
Majinyata takwas sun sha fama da wasu nau'ikan cututtukan thrombosis hade da kananan matakan jini, wanda ke ingiza daskarewar jini.
Babu wani rahoto game da daskarewar jini daga allurar rigakafin Pfizer-BioNTech, in ji mai kula na Burtaniya, inda ta kara da cewa "cikakken bincikenmu a cikin wadannan rahotannin yana gudana".
Amma babban jami'iyar MHRA Dr June Raine ta jaddada cewa fa'idojin da aka samu na allurar ya fi hadarin ta. "Jama'a su ci gaba da karbar allurar rigakafin su idan aka gayyace su don yin hakan," in ji ta.
Barka Da Zuwa Bz News 24/7:
Shin Kana Buqatar Musanar Dakai Zafafan Labaran Abinda Ke Faruwa A Najeriya Dama Duniya Baki Daya Akida Yaushe?
Idan Kana Buqata Kasance Damu a Group Dinmu Na WhatsApp Ta Hanyar Shiga Yanzu👇
https://chat.whatsapp.com/Cl3ssMEUvovLoTJ3ReHz5D
Kasance Cikin Jerin Masu Tayamu Yada Wannan Shafin Kayi Copy Na Adreshin mu Ka yada ga Sauran Al-ummah ga Adreshin 👇
https://www.bzglobalservice.com.ng
0 Response to "Daga Neman gira anrasa Ido: Mutum bakwai 7 sun mutu Bayan anyi Musu Allurar rigafin korona"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?