--
Da duminsa: Rikici ya barke wajen zaben shugabannin PDP a Kaduna,

Da duminsa: Rikici ya barke wajen zaben shugabannin PDP a Kaduna,


Rikici ya barke yayin zaben shugabannin jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP na shiyar Arewa maso yammacin Najeriya ranar Asabar.





Wasu mambobin jam'iyyar sun bayyana rashin gamsuwarsu da yadda akayi tsarin zaben kuma hakan ya sa suka fasa akwatunan zaben kuma suka rikirkita wajen da ake zaben.





An gudanar da taron zaben ne a unguwar Rigachikun ta jihar Kaduna. An cikin hotunan taron, ana iya ganin yadda aka fasa akwatunan zabe kuma aka rikirkita kujeru.









Wasu rahotannin sun nuna cewa an yi musayar kalamai kuma an baiwa hammata iska wanda hakan ya tilasta kawo karshen taron zaben.


0 Response to "Da duminsa: Rikici ya barke wajen zaben shugabannin PDP a Kaduna,"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?