--
Bikin Sallah: Fitilar Dambatta Ta Shirya Tseren Keke Karo Na Biyu

Bikin Sallah: Fitilar Dambatta Ta Shirya Tseren Keke Karo Na Biyu


Mujallar yaɗa labarai a matakin ƙaramar hukumar Dambatta wato FITILAR DAMBATTA ta sake shirya gasar tseren keke a karo na biyu (2) a Karamar Hukumar Dambatta da Makoda.





Da yake magana shugaban kwamitin tsare tsare na gudun tseren, Auwalu Nakarkata Dambatta ya ce, nan bada jimawa ba za'a sanar da lokacin da za'a fara sayar da form din shiga gasar kamar yanda aka yi a baya.





Auwalu ya ƙara da cewa; ana shirya wannan gasa ne domin sada zumunci tsakanin matasa da nishadantar da al' umma da nunawa jama'a mahimmanci motsa jiki ga lafiyar ɗan Adam.





Auwalu ya ƙara da cewa; a wannan karon mun faɗaɗa wasan har zuwa Ƙaramar Hukumar Makoɗa dan kara dankon zumunci da karfafa alaƙa tsakanin matasan yankunan biyu.





A karshe akwai kyaututtuka masu yawa ga wanɗanda suka lashe wannan gasa daga gurbi na daya (1) har zuwa na Uku (3). Sannan akwai shaidar karramawa da za a ba kowane Ɗanwasa. Kwai kyaututtukan da muke sa rai za a samu daga hannun jama'a kamar yanda aka samu a waccan karon. A wannan karon idan an samu da yawa za duba yiwuwar bayar da kyauta har zuwa na biyar (5).








0 Response to "Bikin Sallah: Fitilar Dambatta Ta Shirya Tseren Keke Karo Na Biyu"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?