
Bidiyon Daloli: Jaafar ya ɓoye kansa sakamakon barazana da ya ke fuskanta
Jaafar Jaafar, mawallafin jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a intanet ya boye kansa - Jaafar ya shiga buyan ne saboda abin da ya kira barazana ga rayuwarsa
inda ya ce wasu mutane na bin sahunsa duk inda ya tafi Hakan na zuwa ne bayan rundunar yan sanda ta gayyaci Jaafar domin amsa tambayoyi kan zargin tada fitina da karya
Mawallafin Jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, wanda ya wallafa bidiyon Gandollar, ya tsere daga gidansa ya shiga buya bayan samun sakonnin barazana da dama a cewar PRNigeria.
Hakan na zuwa ne a yayin da ya ke daf da amsa gayyatar yan sanda da ke bincike kan "hadin baki don aikata laifi, bata suna, karya da tada zaune tsaye".
"Rayuwar Jaafar na cikin hatsari duba da cewa wasu mutane da ba a san ko su wanene ba suna binsa a gidansa na Abuja da Kano," PR ta ce ta jiyo wani na kusa da Jaafar yana cewa.
Dan jaridar ya wallafa fayafayen bidiyo na Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano a watan Oktoban 2018, yana karbar daloli da ake zargin cewa rashawa ne daga hannun dan kwangila.
A watan Maris, ya rubuta takardar korafi zuwa ga tsohon Sufeta Janar na 'Yan sandan Nigeria, Mohammed Adamu kan barazana ga rayuwarsa.
Hakan na zuwa ne bayan hirar da BBC Hausa ta yi da Ganduje a ranar 19 ga watan Maris inda ya ce zai dauki mataki kan wadanda suka fitar da bidiyon.
Kafin ya shiga buya, sashin sa ido na IGP na yan sanda ta gayyaci Jaafar domin ya amsa tambayoyi kan zarginsa da tada fitina da yada karerayi.
Ya kamata a gurfana gaban yan sandan ne a ranar 19 ga watan Afrilu. Daily Trust ta yi kokarin ji ta bakin rundunar yan sanda amma bata iya tabbatar da lamarin ba.
Source: Legit
0 Response to "Bidiyon Daloli: Jaafar ya ɓoye kansa sakamakon barazana da ya ke fuskanta"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?