Amfani Da Layin Waya Babisa Ka'ida ba, ya janyowa Mutum biyar Fushin Hukumar Ncc
Hukumar sadarwa ta kasa(NCC)ta tabbatar da kama mutum biyar da ake zarginsu da aikata laifin da ke da alaka da layin waya.
Daraktan yada labarai na Hukumar, Dakta Ikechukwu Adinde, ne ya bayyana haka a cikin Wata sanarwa daya first ga manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, ya ce, an samu nasarar kame mutanen ne sakamakon kokarin da hukumar ke yi na yaki da bata-gari.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, ya ruwaito cewa, Adinde ya ce, runduna ta musamman ce daga wannan hukuma ta kai wannan farmakin kuma ta samu nasarar damke wadannan bata-gari wadanda suka dade suna addabar al’umma. Ya ce, rundunar hadin gwiwar sun kunshi DSS da NSCDC.
An kama wadanda ake zargin ne a yankin Wuse da ke Abuja, wadanda kuma tuni aka mika su ga Hukumar NSCDC da ke Wuse a Birnin tarayya domin ci gaba da gudanar da bincike.
Shugaban sashin gudanar da bincike , Mista Salisu Abduwanda wanda kuma shi ya jagoranci tawagar binciken ya ce, dole a kara kaimi wajen kakkabe bata-garin da ke aikata laifuka ta hanyar amfanui da layin waya.
Ya ce, yin amfani da layin waya ba tare da an yi masa rajista ba laifi, wanda Hukumar ta tanadar masa hukunci mai tsanani.
“Laifi babba yin afani da layin waya ba tare da an yi masa rajista ba, wanda aka tanadar masa hukunci ga duk wanda ya yi taurin kai.
“Duk da cewa, gwamnatin tarayya ta dage dokar hana siyar da sabon layin Waya dayi Masa rajista, to amma dole ya zama an hada layin waya da lambar katin shaidar dan kasa.
“Saboda haka za a ci gaba da gudanar da wannan aiki a Birnin tarayya da dukkan kananan hukumomin da ke fadin kasar nan,” In ji shi.
Abdu ya gargadi wadanda ke yin rajistar layi ba tare da izinin hukuma ba, da su gaggauta bari, in kuma ba su bari ba, duk lokacin da suka shiga hannu za su yabawa aya zakinta.
Rahoton Leadership Ayau
0 Response to "Amfani Da Layin Waya Babisa Ka'ida ba, ya janyowa Mutum biyar Fushin Hukumar Ncc"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?