--
Ahmed Musa zai koma buga wa ƙungiyar Kano Pillars wasa duba dalili>>>

Ahmed Musa zai koma buga wa ƙungiyar Kano Pillars wasa duba dalili>>>


Ahmed Musa, kyaftin na kungiyar kwallon kafa na Nigeria, Super Eagles ya ce yana duba yiwuwar komawa kungiyar Kano Pillars na kankanin lokaci, The Cable ta ruwaito. Tsohon mai bugawa CSKA Moscow gaba baya tare da kowanne kungiya tun bayan rabuwarsa da Al Nassr a watan Oktoban 2020.





A hirar da ya yi da BBC Sports Africa, Musa ya ce ya yi magana da Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano da Shehu Dikko, shugaban kamfanin kula da League, LMC kan yiwuwar bugawa Yaran Masu Gida wasanni kadan.





Tsohon dan wasan na Leicester City ya kuma ce hakan zai taimaka wurin kara fito da gasar na Nigeria a idon duniya sannan zai bashi damar ya rika motsa jiki.





"Bayan magana da gwamna da shugaban LMC, Ina duba yiwuwar buga wa Kano Pillars wasu wasanni," in ji Musa. "Duk abinda zai habaka darajar wasan kwallon kafa a Nigeria abu ne da ya dace in yi kuma Kano pillars na da muhimmin matsayi a zuciya.





"Ita ce kungiyar da ta taimaka min na zama kwararren dan kwallo a yau, don haka akwai alaka mai karfi tsakanin mu fiye da kwallo."






Related Posts

0 Response to "Ahmed Musa zai koma buga wa ƙungiyar Kano Pillars wasa duba dalili>>>"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?