
Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban kasar Chadi, Mahamat Deby
Kun samu labarin cewa 'dan marigayi tsohon shugaban kasa, Idris Deby, ne aka zaba domin ya gajin mahaifinsa saboda shine shugaban majalisar sojojin kasar.
Ga wasu abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban Chadi:
1. Janar-Manjo Mahamat Deby Itno ya fara shiga makarantar Soja ne a kasar chadi
2. Daga baya ya samu horo a kasar Faransa, a makarantar Sojin Aix-en-Provence.
3. Bayan kammala a Faransa, an nada shi matsayin mataimakin kwamandan groupement infenterie.
4. Ya fita yakinsa na farko a Afrilun 2006 lokacin da yan tawaye suka kai hari babbar birnin kasar, daga baya kuma yayi musharaka a yaki a gabashin Chadi tare da Janar Abu Bakr Al Said.
5. Ya jagoranci rundunar Sojojin kasar lokacin yakin Am Dam, inda dakarunsa suka ragargaji yan tawaye.
6. A Junairun 2013, an nada Mahamat matsayin mataimakin kwamandan rundunar Sojoji na musamman a Mali karkashin Janar Oumar Bikimo.
7. A ranar 22 ga Febrairu, ya jagoranci Sojoji wajen yakan yan tawaye a Adrar al-Ifoghas dake Arewacin Mali. Sun samu nasara a yakin amma sun yi rashin Sojoji 26.
8. Bayan yan tawayen FACT sun kashe mahaifinsa ranar 20 ga Afrilu, 2021, Sojoji sun zabesa matsayin shugaban rikon kwarya.
Mahamat Deby zai jagoranci kasar na tsawon watanni 18 yayinda majalisar Soji ke shirin gudanar da zabe.
Source: Legit
0 Response to "Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban kasar Chadi, Mahamat Deby"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?