'Yan Boko Haram da 'yan bindiga masu gwagwarmayar nemawa arewa 'yanci ne, Adamu Garba
Tsohon dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar APC, Adamu Garba ya je kafar sada zumunta inda ya bayyana takaicinsa a kan yadda jama'a ke nuna ra'ayinsu dogaro da yankin mutum.
Garba ya kwatanta mutanen kudancin Najeriya da munafukai, ya ce basu iya kushe duk wani laifi da mutanen yankinsu suka yi amma su dinga kushe na arewa, Vanguard ta wallafa.
"Alamu suna nuna cewa muna da baiwar matsayi, mutunci da kuma arziki kuma muna da masu saka bama-bamai da alburusai a arewa," Garba yace.
"Kun ga munafuncin da ke cike da yadda ake shawo kan matsalolin Najeriya?" A wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter, Garba ya alakanta wasu ayyukan 'yan bindiga da suka hada da satar yara, kai hari kauyuka da kashe-kashe da irin ayyukan Ralph Uwazuruike da Nnamdi Kanu.
Dukkansu suna ikirarin cewa masu gwagwarmaya ne kuma an saka musu da kujerun siyasa, kwangiloli da kuma mayar da su jarumai a yankin kudu maso gabas. Garba yace babu banbanci tsakanin Abubakra Shekau da Nnamdi Kanu da Sunday Igboho.
DAGA BZ NEWS 24/7
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "'Yan Boko Haram da 'yan bindiga masu gwagwarmayar nemawa arewa 'yanci ne, Adamu Garba "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?