Yadda Fasto Ya Saka Ni Na Kashe Mahaifiya Ta Da Adda, Mata Mai Shekara 30 Tayi bayani
Rundunar yan sanda na jihar Ondo ta kama wata mata, Blessing Jimoh, mai shekaru 30 saboda kashe mahiyarta, Ijeoma Odo The Nation ta ruwaito.
Blessing ta ce ta halaka mahaifiyarta da adda bayan fasto ya fada mata cewa mahaifiyar mayya ce.
An yi holen ta tare da wasu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban. An ce faston yanzu ya tsere don gudun kada hukuma ta damko shi.
Blessing ta ce tana yara hudu kuma ta aikata laifin ne a lokacin da suke aiki tare a gona a Ile-Iluji. Ta yi ikirarin cewa hankalinta ya gushe a lokacin da ta aikata laifin.
A cewarta, "Wani abu ne da ke damu na ya saka ni na kashe mahaifiya ta. Ban yi farin cikin abin da na aikata ba.
"Na yanka wutan ta da adda. Fasto ne ya fada min ita mayya ce kuma na tafi in roke ta. Mahaifiya ta yar asalin jihar Enugu ne. Muna ta neman faston amma ba mu gan shi ba."
Kwamishinan yan sanda na jihar Ondo, Bolaji Salami, ya ce za a gurfanar da wacce ake zargin nan bada dadewa ba.
DAGA BZ NEWS 24/7
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Yadda Fasto Ya Saka Ni Na Kashe Mahaifiya Ta Da Adda, Mata Mai Shekara 30 Tayi bayani"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?