Wata uwa mai yara biyu ta mutu yayinda take tsaka da holewa da saurayinta a Yola
Wata mata mai shekaru 37 wacce ked a haihuwar ‘ya’ya biyu ta mutu yayin holewa da masoyinta a Yola, babban birnin jihar Adamawa.
Yan sanda sun kama masoyin nata mai suna Lekan Agboola, wanda ya kasance injiniya a kamfanin sadarwa.
DSP Suleiman Nguroje, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Adamawa, ya ce Agboola, wanda a yanzu haka yake tsare a sashin binciken manyan laifuka na rundunar, yana da mata da yara biyu, suna zaune a Legas.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Agboola ya furta cewa marigayiyar ya kasance budurwarsa fiye da shekaru uku.
Da yake bayanin abin da ya faru a ranar da ta mutu, Agboola ya ce, “A ranar 24 ga Fabrairu, 2021, da misalin karfe 9 na safe, na kira ta a waya na ce ta zo ta gan ni saboda ba mu ga juna ba na wani lokaci.
Lokacin da ta iso, mun fara holewa sai kwatsam ta faɗi. “Lokacin da na fahimci ba ta numfashi, sai na kira daya daga cikin abokaina mata na fada mata abin da ya faru.
Ta shawarce ni da in kai ta asibiti inda aka tabbatar da cewa ta mutu.” Nguroje ya ce ‘yan sanda na kokarin binciken ainihin abin da ya sa matar ta mutu.
DAGA BZ NEWS 24/7
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Wata uwa mai yara biyu ta mutu yayinda take tsaka da holewa da saurayinta a Yola "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?