--
Matashiya 'Yar Kano ta kirkiro Application domin kai rohoton fyade ga hukuma Kai Tsaye

Matashiya 'Yar Kano ta kirkiro Application domin kai rohoton fyade ga hukuma Kai Tsaye


Matashiya haifafar jihar Kano ta ƙera manhajar android na kai rahoton fyaɗe  Sa'adat Aliyu ta ce kowa zai iya Shiga Playstore domin sauke manhajar 'Helpio App'


Matashiyar wacce ta kafa kamfanin Shamrock ta ce tana aiki kan wani manhajar da zai amfani mata da sauran jama'a 


matashiyar ta kasance haifafar jihar Kano, Saadat Aliyu wadda ta ƙera manhajar android mai suna 'Helpio App' domin kai rahoto kan fyaɗe, Channels Television ta ruwaito. An kaɗamar da 'Helpio App' a playstore a ranar 6 ga watan Agustan 2020


Saadat Aliyu wacce ta kafa Shamrock Innovations, cibiyar Fasaha ta Mata da Matasa a Kano ta ce kowa na iya zuwa Playstore ya sauke manhajar a wayarsa. 


"Za ka iya zuwa Playstore, ka nemo shi sannan ka sauke a wayarka. Daga nan sai ka yi rajista da imel ɗin ka cikin harshen Hausa ko Ingilishi," kamar yadda ta shaidawa Channels Television a ranar Litinin. 


"Kawo yanzu kungiyar tallafawa wadanda aka ci zarafinsu, marayu da marasa galihu (ISSOL) da wata ƙungiyar na tallafawa gajiyayu, kare hakkin yara da walwalarsu (EDCRAW) sun yi rajista a manhajar." 


Ta ce ta fara koyon fasahar sadarwa ne daga wurin ɗan uwanta a lokacin tana ajin ƙaramar sakandare daga bisani ta kowa ya kanta har ta zama mai ƙera manhaja. 


Matashiyar ta ce nan ba da dadewa ba za ta ƙaddamar da wata sabuwar manhajar ta mai alaka da fasaha da kuɗi da ake fatan zai taimakawa mata da sauran jama'a. 


DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "Matashiya 'Yar Kano ta kirkiro Application domin kai rohoton fyade ga hukuma Kai Tsaye"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?