
Magidanci ya kashe matarshi saboda koko da kosai na Karin kumallo Duba Abinda Ya faru
Wani matashi dan shekara 20 ya shiga hannun hukumar yan sandan jihar Neja kan laifin kisan matarsa kan sabanin da suka samu kan Kunun karin kumallon da tayi masa.

Bayan sabanin da suka samu, Danladiya bugi matarsa, Zulai Lawal, har ta sume. Daga baya ta mutu a asibiti, rahoton TheNation.
Yayinda aka bayyanashi a hedkwatar hukumar yan sandan jihar dake Minna, Danladi ya bayyana cewa bai taba tunanin matarsa za ta mutu sakamakon bugun ba. Ya ce sun shiga dagawa juna murya ne lokacin da ya nuna rashin jin dadin kunun da tayi masa, kuma daga nan ya shiga bugunta.
"Ban taba tunanin za ta mutu ba. Kawai sabani muka samu kan Kunu kuma ban san lokacin da ta sume ba zata tashi ba. Da na sani ban bugeta ba, ina nadama," yace. Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya ce an damke Danladi ne a kauyen Kadaura dake karamar hukumar Rafi.
Abiodun ya ce an kaddamar da bincike kan lamarin kuma za'a gurfanar da shi a kotu.
0 Response to "Magidanci ya kashe matarshi saboda koko da kosai na Karin kumallo Duba Abinda Ya faru"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?