Kungiyar Inyamurai na neman akama Dr. Ahmad Gumi A bincikeshi duba dalilinsu
Kungiyar matasan Ibo ta 'The Ohanaeze Ndigbo Youth Council, OYC,' ta bukaci a kama malamin addinin musulunci da ke kokarin yin sulhu da yan bindiga a arewacin Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi nan take, rahoton PM News.
Gumi ya fusata kungiyar ta Igbo ne sakamakon kwatanta shugaban Ibo, marigayi Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu da yan bindiga a hirar da aka yi da shi a BBC Pidgin.
Ojukwu ne ya jagorancin kabilar Ibo yayin yakin basasar Nigeria da aka shafe shekaru uku ana gwabzawa wadda ta yi sanadin salwantar miliyoyin rayyuka, kuma na ganin laifin da Ojukwu ya yi ta yi kama da na yan bindiga.
A martaninsa, Mazi Okwu Nnabuike, Shugaban OYC na kasa, ya ce ya yi mamakin yadda har yanzu hukuma ba ta kama Gumi ba. Ya ce duk da cewa akwai alamun Gumi na da 'alakar soyayya' da yan ta'addan, jami'an tsaro sun kawar da kansu sun bar shi yana yawo yayinda tsaro ke cigaba da tabarbarewa a kasar.
OYC cikin sanarwar da ta raba wa manema labarai ta ce, "Nigeria na kan gaba a tarihinta na cigaba da zama kasa daya. Ba a taba samun lokacin da ake tafka laifuka a kasar nan ba da sunan kungiyoyi bayan daban-daban.
DAGA BZ NEWS 24/7
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Kungiyar Inyamurai na neman akama Dr. Ahmad Gumi A bincikeshi duba dalilinsu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?