--
Karshen Duniya akaron farko matar aure ta wallafa bidiyon mijinta yana mata wanka

Karshen Duniya akaron farko matar aure ta wallafa bidiyon mijinta yana mata wanka


A ‘yan kwanakin nan Anita Joseph ta kuma jawo abin magana a kafofin yada labarai da sada zumunta na zamani saboda wallafa wani bidiyo a shafinta. Anita Joseph ta wallafa bidiyon mijinta ya na yi mata wanka, wannan bidiyo ya jawo an dura kan ‘yar wasar, wasu kuma suna ganin hakan ba wani laifi ba ne.


Joseph wanda fitacciyar ‘yar wasar Nollywood ce ta wallafa wannan bidiyo ne a shafinta na Instagram. Duk da cewa Anita Joseph ba ta bayyana tsiraicinta a wannan bidiyo ba, hannuwan mai gidanta sun fito, inda aka fahimci cewa ya na durje mata jiki a kewaye. 


Za a iya ganin ‘yar wasar kwaikwayon ta na wasu maganganu da ba a iya jinta a wannan bidiyo, yayin da ake iya ganin hannuwan mijinta dauke da ruwan wanka. Da ta wallafa bidiyon, Jarumar ta ke cewa: “Yayin da masoyi ya ke taimaka wa aikinta, sai abin abin ya zo maka cikin sauki♀️" 


Wasu sun fito su na kiran jarumar da cewa maras kunya ce, wasu kuwa su ka ce ba ta da aikin yi ne. Zilex_gurl ta ce: “Ba ki tsufa da wannan ba? Ko don jiya-jiya ki ka yi aure? Kin auri yaro da ki ke ta wasa da hankalinsa? Kin tsufa. Ba ki ganin cinyarki da fuskarki ne? Bari ayi ta yaudararki saboda maula.”


Princ_essnaomi: Ya yi tsaki, “Hisssssssss." ya ce “Na tsani wannan mata.” Shi kuwa official_hillsedith cewa ya yi ya kamata 'yar wasar ta Nollywood ta duba kwakwalwarta. Irinsu Ogarblessingblessing gani su ke yi mahassada ne su ke neman taso Joseph da sahibinta a gaba.


Kwanan nan tauraruwar wasan kwaikwayon Kannywood, Hadiza Aliyu wanda aka fi sani da Hadiza Gabon, ta fadi abin da ya fi burge ta a rayuwar Duniya. Fitacciyar ‘yar wasar ta ce ganin mutane su na nuna wa juna kauna, shi ne abin da ya fi burge ta. 


KALLI BIDIYON AKASA: 




 DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "Karshen Duniya akaron farko matar aure ta wallafa bidiyon mijinta yana mata wanka"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?