Karon farko: Gwamnan sokoto ya tuka mota mai aiki da wutan lantarki wadda aka kera a Najeriya -Kalli Hotuna>>>
Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato ya amshi motar Kona mai aiki da Wutar Lantarki wacce Hukumar Kula da kera motoci da cigaban motoci ta kasa (NADDC) tare da hadin gwiwar kamfanin Stallion suka bude kwanan nan.
Ku tuna cewa a ranar 5 ga watan Fabrairu, NADDC, a karkashin jagorancin Darakta-Janar na ta, Jelani Aliyu, ta gabatar da motar mai aiki da lantarki ta farko da aka kera a cikin gida mai suna Hyundai Kona, a Abuja.
Motar an sanya mata farashin Naira miliyan 24 ga kowane daya, tare da ba da garantin batir da kira na tsawon na shekara 5, 100% aiki da lantarki, ba amfani da mai za kuma a iya cajinta a gida da wajen aiki, Daily Nigerian ta ruwaito.
Da yake jawabi bayan gwajin motar a gidan gwamnati na Sakkwato, Gwamna Tambuwal ya yaba da shirin, yana mai bayyana shi a matsayin wani sauyi na al'adu wanda zai shafi rayuwa da kuma damar 'yan Najeriya matuka.
A cewar Tambuwal, yana da kyau cewa yayin da nasarorin kimiyya a duniya ke turawa zuwa daina amfani da mai, Najeriya tana da nasarori irin na fasaha kamar mota mai aiki da lantarki da za ta kawo sauyi kan yadda ake ginin gidaje da kiyaye su, gina hanyoyi, da kuma sarrafa su.
Don haka gwamnan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dauki matakan da suka dace wajen amfani da damar da Jihar Sakkwato ke da shi don tallafawa wajen fadada tattalin arzikin jihar. Tambuwal, wanda ya bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da yake tuka mota mai amfani da lantarki,
ya bayyana fasahar a matsayin mai ban sha’awa da kuma kyakkyawar muhalli, ya kara da cewa fasahar ta fi rahusa ta fuskar kulawa. Gwamnan, yayin bayyana Mista Aliyu a matsayin babban jakadan jihar, ya ba da tabbacin goyon bayan sa ga NADDC a kokarinta na sauya fasalin kamfanin kera motoci na kasar.
Ya kuma yabawa babban daraktan NADDC bisa halartar kasuwar baje kolin, yana mai cewa kasancewarsa ya jawo zuba hannun jari da dama a jihar da yankin. An gabatar da motar a wani baje kolin Kasuwanci na jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara da ke gudana a Sakkwato, shugaban NADDC din dan shekara 55 ne ya gabatar da ita.
Shugaban na NADDC ya kasance tsohon ma'aikaci a America's General Motors wanda ake alfahari dashi don zanen wata mota a 2004 Pontiac G6 da 2010 Chevrolet Volt.
DAGA BZ NEWS 24/7
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Karon farko: Gwamnan sokoto ya tuka mota mai aiki da wutan lantarki wadda aka kera a Najeriya -Kalli Hotuna>>>"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?