--
Kalli yanda wasu mata sukayi zanga zanga jikinsu rabi tsirara a wata jihar kudu>>>

Kalli yanda wasu mata sukayi zanga zanga jikinsu rabi tsirara a wata jihar kudu>>>


A ranar Litinin, 8 ga watan Maris, 2021, wasu mata da-dama a garin Umueri, jihar Anambra su ka yi zanga-zanga da nufin nuna wa gwamnati fushinsu. Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa wadannan mata sun yi zanga-zangar ne da rabin jikinsu a bude, saboda karfa-karfa da gwamnatin jihar za ta yi masu.


Wadannan mata su na zargin gwamnatin jihar Anambra ta Willie Obiano za ta karbe masu filaye domin ta gina filin tashi da saukar jiragen sama a Umueri. Matan da su ka yi wannan zanga-zanga da rabin jikinsu a bude sun yi ikirarin cewa gwamna Willie Obiano ya na kokarin karbe filayensu saboda son rai.


Rahotanni sun ce a irin wannan yanayi na tsiraici, matan su ka taka har yankin da za a yi filin jirgin saman, su ka hura wuta a kan titi, su na tafe su na ihu. Matan nan sun sha alwashin ba za a karbe dukiyar da za su bar wa ‘ya ‘yansu da jikokinsu gado ba. 


Jaridar ta ce cikin masu wadannan zanga-zanga akwai masu kukan cewa gwamnatin Anambra ta na neman wawurar filayen da su ka fi karfin aikin da za ayi. Wata ta rubuta: “Obiano ka koma wa 729.606ha na ainihin filin da aka ware domin ayi aikin filin jirgin.” 


“Kauyukan Enuagu, Umuinu da Umuopu sun ba gwamnati fili har 729ha a lokacin da Chris Ngige yake gwamna, amma Obiano ya karbe karin wasu 1200ha.” Tsoron matan shi ne idan su ka bada filayensu, ba za a samu wurin noma a yankin ba. Duk abin da yake faru wa, gwamnatin Obiano ba ta ce komai ba har yanzu. 


Dazu nan ku ka ji cewa Kungiyar CAN ta taso Gwamna Abdulrahman AbdulRazaq a gaba a kan dokar iznin amfani da Hijab da aka kawo a makarantun Kwara. Gwamnan jihar Kwara ya ce duk wata dalibar da ta ga dama za ta iya zuwa makaranta cikin hijabinta, amma kungiyar CAN ta ce ba za ta yarda da wannan ba. Kungiyar CAN ta zargi Gwamnan da son-kai da rashin adalci, ta bukaci ya janye wannan dokar. 


DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "Kalli yanda wasu mata sukayi zanga zanga jikinsu rabi tsirara a wata jihar kudu>>>"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?