--
Kalli Hotuna: Yansanda sun damke Uwargida da ta kashe Amarya da tabarya
ta kone gawarta

Kalli Hotuna: Yansanda sun damke Uwargida da ta kashe Amarya da tabarya ta kone gawarta


Rundunar yansandan jihar Niger ta kama wata mata yar shekara 24 mai suna Amina Aliyu bisa zargin kashe Amarya da mijinta ya auro a jihar Niger.





Shafin ISYAKU.COM ya ruwaito cewa an kashe Amarya mai suna Amina Aliyu ranar Talata 23 ga watan Maris, inda aka sami gawarta kwance a gidanta kuma rabin jikinta a kone da wuta. An yi zargin cewa an yi amfani da tabarya ne aka kasheta.





R.I.P




Kakakin yansandan jihar Niger DSP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike.





A wata takarda da Abiodun ya sa wa hannu amadadin Kwamishinan yansandan jihar Niger, ya ce :





"Ranar Talata wani mutum mai suna Bello Lawal da ke Gwari Motors Bosso road Minna, ya kawo Kara amadadin Alhaji Aliyu Abdullahi mai shekara 45 da ke zaune a Mandela road Sauka Kahuta, cewa an sami gawar matarsa kuma Amaryarsa mai suna Fati Aliyu jina jina, jikinta kuma a kone da wuta.





R.I.P




"Bayan samun wannan koke ne yansanda suka shiga aiki, kuma suka kama uwargidan mai suna Amina Aliyu yar shekara 24. Yansanda sun sami tabarya da ake zargin Amina ta yi amfani da shi ta kashe Fatima saboda yar uwar Amina ta shaida wa yansanda haka, kuma shaida ce domin a gaban jdonta lamarin ya faru.





R.I.P




Yansanda sun dauki tabarya da ake zargin Amina ta kashe Fatima da shi, kuma za mu gurfanar ta Ammina a gaban Kotu da zarar mun kammala bincike" Inji DSP Wasiu Abiodun.





DAGA BZ NEWS 24/7





Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:





https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7





Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 





Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 





Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice





Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 





bzglobalservicelabari@gmail.com


0 Response to "Kalli Hotuna: Yansanda sun damke Uwargida da ta kashe Amarya da tabarya ta kone gawarta"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?