--
Kalli Bidiyon liyafar biki ana kwashe kudin liki da babban bokiti wanda
ya janyo cece-kuce

Kalli Bidiyon liyafar biki ana kwashe kudin liki da babban bokiti wanda ya janyo cece-kuce


Wasu ma'aurata 'yan Najeriya da har yanzu ba a gane ko su waye ba sun karade kafar sada zumunta da salon da suka bayyana yayin bikinsu.





A wani bidiyo da @iam_steveola ya wallafa, an ga yadda ake ruwan kudi a wani biki da nairori amma ake kwashewa da wata katuwar bokitin roba.





Bidiyon ya nuna zukekiyar amaryar sanye da kayan gargajiya tana zaune yayin da take kallon wasu maza biyu suna kwashe kudin a bokitin roba.





Kalli Bidiyon Qasa:









Har yanzu dai ba a san lokaci ko wurin da aka yi bikin ba. Bidiyon tuni ya samu sama da tsokaci dubu takwas daga ma'abota amfani da Twitter.





Yayin da wasu ke mamakin yawan kudin da aka lika, wasu na nuna mamakinsu ne akan yadda ake kwashe kudin a bokitin roba.





DAGA BZ NEWS 24/7





Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:





https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7





Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 





Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 





Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice





Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 





bzglobalservicelabari@gmail.com


0 Response to "Kalli Bidiyon liyafar biki ana kwashe kudin liki da babban bokiti wanda ya janyo cece-kuce"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?