Kaico: Ta banka wa al'aurar yar shekara 8 wuta da ashana bayan duka da wayan wuta, duba dalili
Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta kama wata matar aure mai suna Aisha Abdullahi Gaide, bisa zargin yi wa diyar kishiyarta dukan cin zarafi da yunkurin aikata kisan kai.
Kakakin yansandan jihar Bauchi SP Ahmed Mohammed Wakil, ya shaida wa manema labarai a wata takarda da ya fitar cewa, ranar Litinin 1 ga watan Maris, Aisha ta yi wa Zahra Abdullahi duka da wayar wuta, kuma ta kyasta ashana tana ci da wuta ta saka wa Zahra a al'aurarta, lamari da ya sa ta sami tsananin kuna a wajen.
Zahra diyar kishiyar Aisha ce kamar yadda wata majiya ta labarta, sai dai kishiyar bata gidan a halin yanzu.
Kazalika Kakakin yansandan ya ce Aisha ta yi wa Zahra wannan duka da azaba ne kawai domin ta yi tuntube da ita lokacin da take kwance.
Aisha na hannun yansanda sashen CIID tana ci gaba da amsa tambayoyi.
DAGA BZ NEWS 24/7
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Kaico: Ta banka wa al'aurar yar shekara 8 wuta da ashana bayan duka da wayan wuta, duba dalili"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?