Jam'iyyar APC Ba Za Ta Dawo Mulki Ba a Shekarar 2023, In Ji SDP
Jam'iyyar Social Democratic Party, SDP, ta yi addu'ar cewa kada Allah ya bawa jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ikon cigaba da rike mulkin kasa bayan babban zaben 2023, The Punch ta ruwaito. Jam'iyyar hammayar ta ce fatan yan Nigeria shine mulkin shugaba Muhammadu Buhari ya zama karshen jam'iyyar APC a kasar.
A hirar da ya yi da wakilin majiyar Legit.ng a ranar Juma'a, Alfa Mohammed, Sakataren SDP na kasa, ya yi kira da sauran jam'iyyu masu irin tunaninsa su hada hannu wuri guda don kawar da APC a babban zaben da ke tafe a 2023.
Shugaban kwamitin riko na kasa na APC, Mai Mala Buni, a ranar Talata ya ce jam'iyyar mai mulki na nufin cigaba da rike mulki na tsawon shekaru 32 nan gaba. A martaninsa kan shirin da APC ke yi don cigaba da mulki har shekaru 32 nan gaba, Mohammed ya ce, "Da farko, Allah kada ya bawa APC nasara a zaben da ke tafe.
"Idan kasa ta tsinci kanta cikin rashin sa'a na samun gwamnati wadda ba ta iya mulki ba kamar APC a yanzu, yana da muhimmanci yan kasar su hada kai domin ganin gwamnatin ba ta cigaba da mulki ba."
SOURCE: LEGIT.NG
DAGA BZ NEWS 24/7
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Jam'iyyar APC Ba Za Ta Dawo Mulki Ba a Shekarar 2023, In Ji SDP"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?