Gwamna El-rufa'i yayi mini abunda bazan taba mantawa dashiba - Sheikh Dahiru Usman Bauchi
BBC Hausa ta yi hira da babban malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi a cikin shirinta na ‘daga bakin mai ita.’ An yi wa fitaccen malamin darikar tijjaniyar tambayoyi da-dama, inda shi kuma ya bada amsoshi.
Daga cikin tambayoyin da aka yi wa Dahiru Usman Bauchi mai shekara 93 a Duniya shi ne abin da aka yi masa da ba zai taba manta wa ba.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce ganin tsufa ta kama shi (kusan shekara 100), ya manta mafi yawan abubuwan da suka faru da shi a rayuwa.
A cewar shehin, abin da ya auku kwanan nan da ba zai manta ba shi ne yadda gwamna ya bada umarni aka shigo gidansa aka dauke masa almajirai.
Dahiru Usman Bauchi ya ce an zo da motoci da bindigogi, aka tattara yaran da su ke koyon karatun Al-Qur’ani a gidansa, da sunan haramta bara.
Ko da cewa Malamin bai kama suna ba, amma gwamnatin Nasir El-Rufai ce ta yi wannan aiki. Dahiru Bauchi ya yi wa gwamnonin kashedin cewa Ubangiji zai yi azaba ga duk wanda ya yi yunkurin yin fito-na-fito da masu karatun Al-kur’ani.
Babban malamin ya ce kamar yadda Allah bai kyale mutanen Annabi Salihu ba, duk wanda ya taba Al-Kur’ani, ba zai gama da Duniya lafiya ba.
A game da sarakunan gargajiya, Shehin ya ce ya fi samun alaka mai kyau da fadar Kano musamman a lokacin Sarki Muhammadu Sanusi I.
A wannan hirar da aka yi da Sheikh Dahiru Bauchi, ya bayyana babban sirrinsa na haddar Al-Kur'ani, kamar yadda aka san shi da baiwar hadda.
Dahiru Bauchi yace iyayensa da kakanninsa ne suka fara samo masu sirri da lakanin haddar Al-kur'ani daga wajen kabilar Bare-bari a kasar Borno. Shehin yake cewa bayan zuwan Sheikh Ibrahim Inyass, ya roka wa mutane saukin yin hadda.
DAGA BZ NEWS 24/7
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Gwamna El-rufa'i yayi mini abunda bazan taba mantawa dashiba - Sheikh Dahiru Usman Bauchi "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?