--
Duba Dalilin daya Sanya Mahaifi Ya Kashe Ɗansa a Kano

Duba Dalilin daya Sanya Mahaifi Ya Kashe Ɗansa a Kano


Kano State Nigeria




Yan sanda a Kano sun tabbatar da kama uban da ya kashe ɗansa ta hanyar lakada masa duka saboda zarginsa da sata Yan sandan sun ce ana tsare mahaifin an tura shi sashin binciken manyan laifuka bangaren kisan kai ana bincike,





Mahaifiyar yaron, wadda ta dade ta rabuwa da mahaifin ta bayyana yadda yaron ya zo mata cikin mawuyacin hali





Wasu da abin ya faru a kan idonsu sun bayyana yadda wani ya yi yunkurin hana mahaifin dukan yaron amma bai yi nasara ba.





Rundunar yan sanda a jihar Kano ta ce tabbatar da kama wani magidanci da ake zargi da halaka dansa mai suna Auwalu Awaisu mai shekaru 19 sakamakon lakada masa duka a ranar Juma'a na makon da ta gabata.





Yan sandan sun ce Auwalu ya riga mu gidan gaskiya a ranar Litinin a Asibitin Murtala da ke Kano sakamakon dukn da mahaifinsa ya yi masa a ka da cikinsa, kamar yadda BBC ta ruwaito a shafinta Na Tiwita









Mahaifin ya yi wa dansa duka ne kan zarginsa da sace masa kaya a shago Acewar wani da al'amarin ya faru a kan idonsa, usamn kabiru yace suna zaune suka ga mahaifin yana dukan yaronsa amma basu san dalili ba kuma ba tafi sun taimaka masa ba ganin abu ne tsakanin da da mahaifinsa





"Muna zaune a cikin shago a nan wurin sai muka ji yana dukan yaronsa a cikin shago, sunan shi Auwalu amma an fi saninsa da Abba, mun tsaya a waje a nan wurin yana ta dukan yaron badai wanda ya je wurin sai makwabcinsa mai wankin hula, ya zo ya same shi, ya ce mishi …





ya dai masa magana, ni banji abinda ya fada masa ba, amma na ji lokacin da shi mahaifin ya ke masa tsawa ya ke ce masa ya fita masa a shago, ganin haka yasa muma ba mu tafi wurin ba," a cewar Kabiru





Hajiya Goshi Muhammad, mahaifiyar yaron wadda ta dade da rabuwa da mahaifin tsawon lokaci ta ce yaron ya zo mata cikin mawuyacin hali ta tambaye shi abinda yafaru, sai ya fada cewa mahaifinsa ne ya doke shi saboda wai bai ga 'mansa ba guda biyu'.





Yaron ya shaidawa mahaiyarsa cewa mahaifinsa ya yi ta dukansa a kai da ciki duk da cewa ya fada masa ba shine ya sace kaya a shagon ba.





Rundunar yan sandan Kano ta bakin kakakinta ya ce mahaifin yaron yana hannunsu,an mika shi sashin binciken manyan laifuka, bangaren kisar kai ana cigaba da bincike a kansa.






0 Response to "Duba Dalilin daya Sanya Mahaifi Ya Kashe Ɗansa a Kano"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?